Ma’aikatar Albarkatun ruwa ta jihar Kano ta Barranta kanta da zargin da ake yi na wata takarda dake yawo a shafukan sada zumunta na ‘social media’ cewa kwamishinan ma’aikatar Ali Haruna Makoda, ya bada umarnin cefanar da wani injin ban ruwa dake madatsar ruwa ta karefa cikin karamar hukumar Tudun Wada.

Daraktan dake kula da noman rani da madatsun ruwa na ma’aikatar Adamu Chiroma ne ya shaida hakan, cikin wata ganawa da yayi da manema labarai.

Adamu Chiroma na cewa kwamishinan Ali Haruna Makoda bai da masaniya kan wannan takarda da aka rubuta, wadda ke nuna yadda ya bada umarni don aiwatar da wannan aiki.

Gwamnatin Kano ta musanta zargin siyar da wani injin dake matatar ruwa ta T/Wada
Politics & Governance · Gwamnatin Kano ta musanta zargin siyar da wani injin dake matatar ruwa ta T/Wada

Chiroma ya kara da cewa, hakan na zuwa kuwa bayan da kwamishinan ya samu rahoton matakin wanda Daraktan mulki na ma’aikatar Abubakar Gambo ya dauki gabarar yi.

“Abin mamakin shi ne yadda har suka karbi kudi kimanin Naira dubu dari biyar a matsayin kafin alkalami, wanda daga baya suka tsara karbar cikon kudin bayan an kunto wannan inji.

“Haka zalika kamar yadda muka fada tun da fari, wanda cin amanar aiki ce da muka kama wannan Darakta da yi, wasu tsiraru da suka taimaka masa wajen aiwatar da hakan”, a cewar Adamu Chiroma.

Tuni dai kwamishinan ma’aikatar albarkatun ruwa na jihar Kano, Ali Haruna Makoda ya umarci jami’an ‘yan sanda da su fadada bincike don hukunta wadanda aka samu da hannu cikin wannan almundahana.

Kano Emerge Champions of PARA Amputee Football

KNSG Approves 1st Term Vacation for Schools

See Also

Chinyere Okonkwo
Author
Chinyere Okonkwo is a political reporter covering Nigerian federal and state governance, elections, and the activities of the National Assembly. Based in Abuja, she tracks policy developments, political party dynamics, and the work of oversight institutions such as EFCC and INEC.

Chinyere has covered three general election cycles and reported on constitutional reform debates, security legislation, and the governance challenges facing Nigeria's 36 states. She holds a degree in political science from Ahmadu Bello University.