Daga Abubakar Abba, Kaduna
A yayin da a gobe Asabar ake shirin gudanar da zabukan kananan hukumomi a jihar Kaduna, Jam’iyyar NNPC reshen jihar Kaduna ta ankarar da musamman mata masu jefa kuri’a, illar sake karbar Taliya.
Sakataren jam’iyyar reshen jihar Bello Ibn Aminu bayyana haka a taron manema labarai da jam’iyyar ta shirya a jihar.
Ya yi nuni da cewa, sanadiyyar karbar taliya a zabukan da aka gudanar a baya a jihar, hakan ya janyo jefa rayuwar wadanda suka karbi taliyar da ma wadanda ba su karba ba, a cikin kangin talauci da haddasa rashin tsaro, musamman a Kaduna.
Karanta Wannan:
Gwamnatin Kano ta musanta zargin siyar da wani injin dake matatar ruwa ta T/Wada
Ya ce, ya kamata masu kada kuri’a a lokacin zaben, na gobe, musamman mata su yi karatun ta nutsu wajen kaucewa kwadayin karba Taliya daga gun yan takara don su zabe su.
Sakataren ya ce, idan masu jefa kuri’a a jihar suka zabi yan takarar NNPP a zaben, za su samar da shugabanci na gari, wanda yasha ban ban da jim’iyyar dake rike da madafun iko a jihar, musammana a bangaren samar da ilimin zamani mai ianganci da kuma inganata rayuwar jama’a.
Ita ma a nata jawabin a wajen taron na manema labarai, shugabar Mata ta jam’iyyar Hajiya Safiya Mu’azu ta bukaci iyaye, musamman mata kar su bari yan siyasa su amfani da yayansu wajen ba su kayan maye don su haddasa rikici a lokacin zaben.