Kungiyar tsoffin daliban KASSOSA kwalejin kimiyya ta Dawakin Kudu aji na 1988 ta gudanar da taron liyafar cin abinci a wani mataki na karfafa zumunci tsakanin mambobin kungiyar.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwar bayan taro da kungiyar ta fitar, wacce sakataren kungiyar Alhaji Hassan Abdulhamid Hassan ya sanyawa hannu kana aka rabawa manema labarai.
Karanta:
Gwamnatin Kano ta musanta zargin siyar da wani injin dake matatar ruwa ta T/Wada
Sanarwar ta kara da cewa, yayin taron dai kungiyar ta dauki gabarar samar da littafi mai dauke da hotuna da bayanan mambobinsu, inda tuni kwamitin da aka dorawa nauyi karkashin Malam Ibrahim Ahmad suka fara ayyukan su.
Haka zalika mambobin da suka sami halartar taron sun dauki hotunan tarihi tare da sauran ‘yan uwan su da suka yi karatu a kwalejin kimiyya ta Dawakin Kudu kuma suka kamala tare.