Close Menu
Good Evening Nigeria…Breaking news in Nigeria
  • News
  • Entertainment
  • Kano
  • International
  • Politics
  • Security
  • Sports
  • More
    • Crime
    • Education
    • Finance
    • Health
    • Kaduna
    • National
    • Nigeria
    • Profile
    • Strategy
    • Technology
Facebook X (Twitter) Instagram
Facebook X (Twitter) Instagram
Good Evening Nigeria…Breaking news in NigeriaGood Evening Nigeria…Breaking news in Nigeria
  • News
  • Entertainment
  • Kano
  • International
  • Politics
  • Security
  • Sports
  • More
    • Crime
    • Education
    • Finance
    • Health
    • Kaduna
    • National
    • Nigeria
    • Profile
    • Strategy
    • Technology
Good Evening Nigeria…Breaking news in Nigeria
Sama da dalibai miliyan 1.2 ne suka amfana da gyara da fadada makarantun sakandare a jihar Kano
Hausa

Sama da dalibai miliyan 1.2 ne suka amfana da gyara da fadada makarantun sakandare a jihar Kano

Umar Idris ShuaibuBy Umar Idris ShuaibuFebruary 3, 2024No Comments2 Mins Read
Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr Email
Share
Facebook Twitter LinkedIn Pinterest Email

Shirin AGILE Kano yana samun ci gaba wajen inganta ilimin yara mata masu tasowa a yankuna birni da karkara .

Babban Jami’in dake kula da ayyukan AGILE a jihar Kano Nasir Abdullahi Kwalli shine ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a kano.

Nasir Kwalli ya ce babban makasudin shirin shi ne magance matsalolin da suka addabi makarantun Sakandare, musamman ga yara mata, wadanda dayawansu ke fuskantar matsaloli kamar rashin isassun makarantu a yankunansu, kayayyakin more rayuwa, ruwa,da tsaftar muhalli.

Karanta:

Najeriya ta zargi kasar Mali da tursasa Matasan kasarta zanga-zangar nuna goyon bayan kasar na ficewa daga ECOWAS

Yace Idan har da gaske kuke son ganin an samu ci gaba a cikin al’umma, to sai kun fara da tarbiyyar ‘yan mata domin su ne uwayen gobe, idan kuna da dimbin ‘yan mata masu ilimi za a samu sauki wajen yada Ilimi ga kowa da kowa.

Domin cimma wannan buri, kungiyar AGILE Kano Project ta fara daukar matakai kai tsaye, kamar gina sabbin kananan makarantu da manyan makarantun gaba da sakandare a yankunan karkara a Kano, samar da ruwan sha da gina bandakai ga ‘yan mata a makarantun sakandare, da baiwa makarantu tallafi da gyara abubuwan more rayuwa da suka lalace.

A cewar Kwalli, Izuwa yanzu an gyara makarantun sakandire 1,228 kuma ana ci gaba da kirgawa.

Ya kuma ce kimanin dalibai 1,269,673 ne suka amfana kai tsaye daga aikin AGILE kuma Ana kan fadada aikin.

“Babu wata al’umma a Kano da ba za ka iya samun aikin AGILE ba, kuma wannan shi ne mafari, wannan kadan ne, da yawa kuma suna tafe nan ba da dadewa ba.” Inji Nasir kwalli.

Bankin Duniya ne ke daukar nauyin shirin na AGILE Kano, kuma Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano tare da hadin gwiwar masu ruwa da tsaki ne ke aiwatar da shi.

Wannan aiki dai na da nufin kara samun daidaiton ilimin makarantun gaba da sakandire tare da inganta karatun da rikon amana a makarantun sakandaren jihar Kano.

Spread the love
Share. Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr Email
Umar Idris Shuaibu

    Related Posts

    Najeriya ta musanta Zarge-Zargen Zagon Kasa da Hukumomin Nijar ke yi Mata

    December 24, 2024

    Zaben Kananan Hukumomi A Kaduna: Jiki Magayi In Kuka Sake Karbar Taliya – Sakon NNPP Ga Masu Kada Kuri’a

    October 18, 2024

    KASSOSA Aji na 88 sun yi taron liyafar cin abinci, sun sha alwashin karfafa zumunci tsakanin mambobi

    July 1, 2024

    Najeriya ta zargi kasar Mali da tursasa Matasan kasarta zanga-zangar nuna goyon bayan kasar na ficewa daga ECOWAS

    February 1, 2024
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    Latest Posts

    Natasha’s Case: ”Senate must remain impartial in handling harassment allegations” – NBAWF

    March 9, 2025

    Hon. Bala Congratulates Ganduje on Tenure Elongation as APC National Chairman

    February 28, 2025

    LG Staff Urged to Remain at Duty Posts to Drive Development

    February 25, 2025

    BREAKING: Lucky Aiyedatiwa Sworn In As Ondo Governor

    February 24, 2025

    El-Rufai Reacts To Tinubu’s Birthday Message

    February 24, 2025
    Advertisement
    © 2025 Good Evening Nigeria
    • Home
    • About Us
    • Contact us
    • Privacy Policy

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.