Mustapha Muhammad Kankarofi
Gwamnatin Najeriya tayi zargin kasar Mali da tursasa wa Matasan kasarta, wajen yin zanga-zangar nuna goyon bayansu, game da ficewar ƙasar daga kungiyar ECOWAS.
Wasu bayanan sirri da manema labarai suka samu ta cikin wata takarda na nuna cewa gwamnatin Mali ta sanya jami’anta na tilastawa ‘yan kasar, su goyi bayan ficewar da kasar tayi daga Ƙungiyar ECOWAS.
Labarai masu alaka:
Najeriya ta bayyana rashin jin dadi da ficewar wasu daga cikin mambobin ECOWAS
Haka zalika cikin bayan da manema labarai suka samu yace “Gwamnatin Mali, ta hannun Ministan Matasa da Wasanni, ta yi kira ga jama’a da su hada kai don goyon bayan shawarar ta kasar dama takwarorinta Burkina Faso da kuma Nijar na janyewa daga kungiyar ECOWAS.
Idan dai za’a iya tunawa, Mali, Burkina Faso da Nijar sun sanar da cewa, sun aikewa da kungiyar ECOWAS, sanarwar ficewarsu daga kungiyar, bayan shafe tsawon lokaci ana taƙaddama a tsakanin ɓangarorin biyu.
Hukumomin sojin kasashen uku sun sanar da shirin ficewa daga kungiyar ta raya tattalin yammacin Afirka, bayan sunyi zargin ana yi musu barazana ga ikonsu, duk da tuni kungiyar ta Ecowas ta nuna rashin jin dadin ta, bisa ficewar kasashen uku daga kungiyar.