Site icon Good Evening Nigeria…Breaking news in Nigeria

Najeriya ta bayyana rashin jin dadi da ficewar wasu daga cikin mambobin ECOWAS

Mustapha Muhammad Kankarofi – Kano

Najeriya ta bayyana bakin cikinta dangane da sanarwar da kasashen Nijar, Mali da Burkinafaso suka dauka na ficewa daga kungiyar hadin kan kasashen Afrika ECOWAS.

Najeriya wadda take zama babbar Jigo da ma rikon shugabancin ECOWAS ta dage wajen ganin an dawo da mulki hannu farar hula tare da sakin hambararren tsohun shugaban kasar Nijar Bazoum Muhammad.

Najeriya ta Kasan ce tana tuntubar dukkan kasashen dake cikin kungiyar ECOWAS domin warware matsalolin da ake fuskanta a kasashen da akayi juyin mulki.

Karanta:

Gwamnatin Kano ta musanta zargin siyar da wani injin dake matatar ruwa ta T/Wada

haka zalika Najeriya na ci gaba da bude kofa ga kasashen Burkina Faso, Mali da Nijar, ta yadda daukacin al’ummar yankin za su ci gaba da cin moriyar tattalin arziki da kimar dimokradiyya da kungiyar ECOWAS ta amince da su.

Najeriya ta kara yin kira ga kasashen duniya da su ci gaba da bayar da goyon baya ga kungiyar ECOWAS da kuma hadin gwiwa da hadin kai.

Sa hannun: Francisca K. Omayuli (Mrs) Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya.

Spread the love
Exit mobile version