Site icon Good Evening Nigeria…Breaking news in Nigeria

Gawuna ya bawa ‘yan wasan Kano dubu dari yayin da gwamnatin Kano ta gaza biyan kudaden gudanar da wasannin PARA

Ahmad Hamisu Gwale – Abuja

Gwamnatin Kano ta gaza bayar da kudaden Alawus-Alawus ga tawagar da ke wakiltar jihar a gasar cin kofin masu bukata ta musamman ta kasa.

Gasar Masu Bukata ta musamman ta kasa ta wannan shekarar, na ci gaba da gudana a birnin tarayya Abuja da kawo yanzu haka kwana biyu ya rage ayi bikin karkare gasar.

Karanta:

Gwamnatin Kano ta musanta zargin siyar da wani injin dake matatar ruwa ta T/Wada

An dai tsara gasar zata gudana daga 8 zuwa 14 ga Disambar shekarar da muke ciki a filin wasa na Moshood Abiola dake birnin tarayya Abuja.

Wakilinmu ya bamu Labarin cewa wasu cikin wakilan ma’aikatar wasanni, da tawagar Yan Jaridu suna ci gaba da shan wahala sakamakon gaza fitar da kudaden Alawus-Alawus din.

Tin a ranar Asabar aka sanarwa tawagar da zasu wakilci Kano a gasar cewa kudaden gudanarwar ta su zai samu jinkiri zuwa ranar Litinin.

To sai dai yau Laraba da aka shiga kwanaki na biyar babu wani yunkuri daga Gwamnatin jihar Kano kan kudaden da ya kamata a saki domin samun damar gudanar da gasar.

Hakan ta sanya Yan Jaridu da Wakilan ma’aikatar wasanni da kansu suke ciyar da kansu, bayaga yadda suke fuskantar barazana abubuwan yau da kullum domin su gudanar da rayuwarsu.

Wani da ya bukaci a sakaye sunansa ya ce hatta Kundin da Gwamna Abba Kabiru Yusuf ya sanya hannu domin amincewa da sakin kudaden gudanarwar na tawagar ya bata, batare da sanin ina ya shiga ba.

Babu wani yunkuri da aka samu daga Gwamnatin jihar Kano kawo wannan lokaci, domin kawowa tawagar dauki bayan da ya rage Kwanaki a karkare gasar ta wannan shekarar.

To amma Shugaban hukumar wasanni ta jihar Kano Alhali Bala Ya ce suna bakin kokarinsu kan wannan batu, yana mai bayar da tabbacin za suyi duk mai yiwa domin tawagar su samu dauki na gaggawa.

A gefe gudama tsohon Mataimakin Gwamnan Kano Nasiru Yusuf Gawuna da ya samu wakilcin Kabiru Ali Mazadu ya baiwa wasu yan wasan tawagar kyautar Kudi Naira Dubu Dari (100,000).

Gawuna wanda ya bayar da kyautar kudin jim kadan bayan kammala wasan karshe da yan wasan Kwallon guragu na Kano Pillars da yan wasan Pillars Amputee suka samu nasarar lashe Sarkar Zinare a gasar.

Haka Zalika Shima dan kwamitin gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars Alhaji Naziru Wapa, ya bai wa yan wasan Kano Pillars na Para-Soccer da na Pillars Amputee kyautar Naira Dubu Hamsin (50,000).

Spread the love
Exit mobile version